Connect with us

Addini

Gwamna Abba Kabir ya ziyarci Alhazan Kano a Saudiyya

Published

on

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya kai ziyarar Sallah ga Alhazan jihar a masaukinsu da ke kasar Saudiyya, inda ya bai wa kowane mahajjaci kyautar Riyal 250, kwatankwacin Naira 105,000.

Gwamnan ya kai ziyarar ne a daren ranar Asabar.

Da yake jawabi yayin ziyarar, Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya yaba da nasarar aikin Hajjin bana da aka samu, inda ya bayyana shi a matsayin wanda ya fi na shekarun baya, musamman na bara.

Gwamnan ya bayyana cewa ziyarar na da nufin karfafa alaka da yin addu’o’i ga jihar Kano da Najeriya, da kuma mika gaisuwa ga mahajjata a bikin Sallah.

Ya kuma ce, Kano da Najeriya ma suna bukatar addu’a, don haka ya nemi Alhazan da su yi addu’o’i na musamman.

Gwamnan ya jajanta wa iyalan mahajjatan da suka rasa rayukansu a Makkah da Madina, da kuma lokacin Arafah, inda ya yi addu’ar Allah ya jikan da wadanda suka rasu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!