Labarai
Gwamna Abba ya bayar da diyar gonaki ga wasu al’umma a kano
Gwamnatin jihar Kano ta ƙaddamar da bayar da diyar gonaki ga al’ummar yankin rijiyar gwangwan, Ƴar gaya dake ƙaramar hukumar Dawakin kudu Sai kuma Lambu, unguwar Rimi dake ƙaramar hukumar Tofa domin basa hakkin su da zasu sami damar zuwa shu cigaba da gudanar da Rayuwar su cikin nutsuwa.
Gwamnan jihar Injiniya Abba Kabir Yusuf ne ya jagoranci bayarwa da diyar a yau Litinin a ɗakin taro na Afrika House dake fadar gwamnatin jihar.
Da yake bayar da diyar gonakin Gwamnan jihar Injiniya Abba Kabir Yusuf ya tabbatar da cewa dukkannin wasu gonaki da gwamnati ta karɓa domin mayar da su alƙarya gwamnatin sa zata tabbatar da biya dukkannin mamallaka guraren haƙƙin su.
Gwamna Yusuf ya ƙara da cewa ganin yadda al’umma suke ƙaruwa a faɗin jihar Kano ya zama wajibi gwamnati ta ƙara samar da guraren da al’umma zasu zauna domin gudanar da rayuwar su cikin nutsuwa da kwanciyar hankali.
Gwamnan ya ƙara da cewa yayin karɓar gonakin anyi duba da yanki da suke da ƙaracin ci gaba shiyasa gwamnati ta zaɓi yankunan nasu domin zamanantar da su wajen zama cikakkiyar alƙarya kamar yadda cikin birni take da shi.
Malan Sani Abba gudane cikin jagororin rijiyar gwangwan yayi ƙarin haske kan yadda suka karɓi wannan diyar inda yayi godiya a madadin su domin gwamnatin Kano ta taimake su
Haka kuma gwamna Abba Kabir Yusuf ya tabbatarwa da al’ummar da suke wannan yankunan cewa duba da yanayi na damina da ake ciki a yanzu gwamnati bazata fara aiki ba sai bayan an cire anfanin gona domin gujewa lalata musu.
You must be logged in to post a comment Login