Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Za mu gyara dukkannin makarantun firamare da sakandare dake kano-Gwamna Abba

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ce a cikin wannan watan zata fara aikin gyara dukkan nin makarantun firamare da sakandare dake faɗin jihar domin bayar da ingantaccen ilimi ga al’umma.

Gwamnan jihar Injiniya Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana hakan da yammacin yau yayin da sarkin ƙaraye Alhaji Dakta Ibrahim Abubakar na biyu ya kawo masa ziyara cikin wani ɓangare na bikin sallah ƙarama.

Gwamnan Yusuf ya kuma ce muhimmancin ilimi tun daga tushe ya sanya gwamnatin sa ta mayar da hankali wajen ingata ilimin firamare da sakandare da samar musu da ingantattun malamai.

A nasa ɓangaren sarkin ƙaraye Alhaji Ibrahim Abubakar na biyu ya ɓukaci gwamnatin Kano da ta gyara musu wasu hanyoyi da suke a yankin na ƙaraye domin samarwa da al’ummar yankin saukin tafiye-tafiye.

Haka kuma gwamnatin kano ta ce zata mayar da hankali wajen inganta rayuwar al’ummar wajen samar musu hanyoyi da sauran abubuwan more rayuwa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!