Labarai
Gwamna Abdullahi Sule ya gabatar da kasafin kuɗin 2026

Gwamnan Jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule, ya gabatar da kasafin kuɗi na shekarar 2026 da ya kai kimanin Naira biliyan 517 da miliyan 540 ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa.
A yayin gabatar da kudirin, Gwamnan ya ce kasafin ya mayar da hankali ne kan ci gaba mai ɗorewa, tabbatar da tsaro, inganta fannin ilimi sai lafiya da kuma bunƙasa tattalin arzikin cikin gida domin amfanin al’ummar jihar ta Nasarawa.
Majalisar dokokin jihar ta tabbatar da karɓar kudirin, tare da alƙawarin nazari kan sabon kasafin kafin amincewa da shi.
You must be logged in to post a comment Login