Connect with us

Labarai

Da dumi-dumi : Ganduje ya aikewa majalisa takardar gabatar da kudirin kasafin kudi

Published

on

Gwamnatin Kano ta aikawa majalisar dokoki ta jihar Kano takardar neman sahalewar ta wajen gabatar da  kudirin kasafin kudin badi a gobe Talata.

Tun a ‘yan kwanakin da suka gabata ne Gwamnan jihar Kano Dr, Abdullahi Umar Ganduje a ya yin zaman majalisar zartarwa ta jiha ya bayyana cewar gwamnati zata gabatar da kudirin kasafin kudin badi a yau Litinin 26 ga watan Okotoba.

Sai dai a ya yin zaman majalisar dokokin ta Kano da safiyar yau ta bayyana cewar gwamnatin Kano ta aikemata da takardar neman sahalewar gabatar da kudirin kasafin kudin badi a gobe Talata.

Shugaban majalisar dokoki ta Kano Abdul’aziz Garba Gafasa ne ya karanta takadar a  kwaryar majalisar ya yin zaman da take yi a halin yanzu.

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 334,784 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!