Labarai
Gwamna Adeleke ya kare matakinsa na yin sauyin sheka

Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, ya kare matakin da ya ɗauka na ficewa daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar AP, da ya ce ya sauya sheƙa ne domin kare kan sa da kuma tabbatar da zaman lafiyar jihar.
Ta cikin wata hirar sa da gidan talabijin na Channels a jiya Laraba, gwamnan ya ce bai yi watsi da PDP , wacce har yanzu yake girmamawa, sai dai ya zaɓi fifita ɗorewar ci gaban da ake samu a jihar ta Osun.
Adeleke ya shiga jam’iyyar AP ne a ranar Talatar da ta gabata bayan ya fice daga PDP, jam’iyyar da ta bashi mulki a zaɓen gwamnan jihar na 2022.
A ranar Laraba ne ya samu tikitin takarar gwamna a karkashin sabuwar jam’iyyarsa ta AP, da a yanzu haka zai kara da ‘yan takara daga APC, PDP, da kuma jam’iyyar haɗaka ta ADP a wani zabe da ake sa ran zai kasance mai matukar tasiri ga makomar siyasar sa
You must be logged in to post a comment Login