Labarai
Gwamna Ademola Adeleke ya fice daga jam’iyyar PDP

Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, ya sanar da ficewar sa daga jam’iyyar PDP, mai adawa ta kasa.
Adeleke ya sanar da hakan ne ta shafin sa na X a daren Litinin, inda ya wallafa kwafin takardar murabus dinsa mai dauke da kwanan wata 4 ga Nuwambar, 2025.
A cikin takardar, Adeleke ya bayyana rikicin da ke faruwa a jam’iyyar a matsayin dalilin ficewa rsa, da ya sa yanke shawarar a yanzu haka.
Gwamnan ya gode wa jam’iyyar bisa damar da ta bashi ya yi aiki a matsayin Sanata mai wakiltar Osun ta Yamma wato West 2017–2019 da kuma Gwamnan jihar Osun.
Sai dai har kawo yanzu Adeleke dai bai bayyana jam’iyyar da zai koma ba bayan barin PDP.
You must be logged in to post a comment Login