Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Coronavirus

Gwamna Badaru ya tsawaita “Lock Down” a garin Kazaure

Published

on

Gwamnatin Jihar Jigawa ta kara tsawaita dokar zaman gida a karamar hukumar kazaure na tsawon mako guda, bayan karewar wa’adin farko da gwamnatin ta sanya.

Shugaban kwamatin yaki da yaduwar cutar kuma kwamamin shinan lafiyar jihar Jigawa Dr. Abba Umar ne ya bayyana haka a Dutse, yayin da yake ganawa da manema labari.

Dr. Abba yace daukar Wannan mataki ya biyo bayan rashin fitowar sakamakon gwajin da suka aika Abuja na mutanan da sukayi mu’a mala da mai dauke da cutar Corona Virus da aka samu a karamar hukumar kazaure cikin makon daya shude.

Kazalika Kwamin shinan yace akwai hadari a saki gari ba tare da sanin makomar lafiyar mutanan da sukayi harkoki da mutumin dake dauke da cutarba.

Koda yake muna iya dakatar da dokar kafin cikar wa’adin na mako daya amma har sai wancan sakamako da muka aika ya fito babu mai dauke da cutar cikinsu gaba daya.

Dr. Abba ya kuma kara da cewa gwamnatin jihar jigawa, ta fara shirin kara raba kayan tallafin abinci ga magidanta, daga cikin kayan gudummawar da jihar ke samu daga kamfanoni da kungiyoyi dama daidai kun al umma.
Daga karshe ya yabawa al ummar kazaure bisa yadda suke bin doka sau da kafa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!