Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Coronavirus

Wasikar Kwankwaso bata bi hanyar zuwa wurin shugaban kasa ba –Bashir Ahmad

Published

on

Mai taimakawa shugaban kasa Muhammadu Buhari kan sabbin kafafan sadarwa na zamani Bashir Ahmad ya ce wasikar da Kwankwaso ya rubutawa shugaban kasa bata bi hanyar da ta dace ba domin isa ga shugaban kasa ba.

Bashir Ahmad ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa, “wannan wasika ce zuwa ga shugaban kasa, ko kuma budaddiyar wasika ce ga mutanen Twitter? na san Injiniyya Rabi’u Kwankwaso a matsayinsa na tsohon gwamna ya fimu sanin sahihiyar hanyar aikawa da shugaban kasa wasika…

A safiyar litinin dinnan ne dai tsohon gwamnan Kano Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso ya aike da wata wasika zuwa ga shugaban kasa kan halin da ake ciki a jihar Kano.

Cikin wasikar Kwankwaso yayi kak-kausar suka ga gwamnatin tarayya kan ta gaggauta kara daukan matakan kariya a jihar Kano, sannan ya nemi da gwamnatin tarayya ta samarwa da jihar Kano cibiyoyin gwajin cutar Corona akalla guda biyar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!