Labarai
Gwamna Dauda Lawal ya kaddamar da sabbin motocin Sufuri

Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal, ya kaddamar da sababbin motocin bas guda hamsin na kamfanin sufuri na jihar.
A wajen bikin kaddamarwar wanda aka gudanar, Gwamna Lawal ya bayyana wannan ci gaba a matsayin cikar alkawari da kuma gado na nagarta, ya na mai cewa hakan na nuna kudirin gwamnatinsa wajen gina jihar a kan turbar ci gaba da kwarewa.
Gwamnan ya kuma ce, samar da motocin bas din zai taimaka wajen inganta harkokin sufuri da rage cunkoson fasinjoji tare da samar da sauki ga matafiya.
Haka kuma, ya yi kira ga mazauna jihar da su kula da kayayyakin da gwamnati ke samarwa domin su ci gaba da amfanar jama’a na tsawon lokaci.
You must be logged in to post a comment Login