Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Gwamnonin Arewa maso Yamma sun tsara hanyoyin da za a bi don ci gaban yankin

Published

on

Amincewa da Samar da Cigaba ta hanyar Noma, Tattalin Arziki da Tsaro A kokarin samar da ci gaba mai dorewa da wadata tattalin arziki, gwamnonin jihohin Arewa maso Yamma sun amince su hada kai da juna domin amfanin yankin

Gwamnonin sun bayyana hakan ne bayan wani taro da suka gudanar a yau Talata a gidan gwamnatin Katsina da ke jihar Katsina

Taron wanda ya samu halartar gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf, gwamnan jihar Zamfara Alhaji Dauda Lawal, gwamnan jihar Kebbi Kauran Gwandu, Gwamnan jihar Sokoto Alh. Ahmed Aliyu, gwamnan jihar Jigawa wanda ya samu wakilcin mataimakinsa da gwamnan jihar Katsina Dr. Dikko Umaru Radda wanda ya kasance mai masaukin baki

Yayin da suke jawabi ga manema labarai na hadin gwiwa jim kadan bayan kammala taron, gwamnonin sun amince da samar da wata manufa guda domin tinkarar kalubalen tsaro da ya addabi yankin a shekarun baya

Haka kuma an amince da yin aiki tare wajen inganta fannin noma ta hanyar inganta harkar shigar da kayayyakin amfanin gona da kasuwannin kayayyaki

Gwamnonin sun kuma tsara hanyar samar da ci gaban tattalin arzikin yankin tare da cikakken tsari na hanyoyin da gwamnatocin jihohin ke amfani da su a kan albarkatun kasa, na zahiri da na dan Adam na jihohin Arewa maso Yamma

“Muna so mu yi amfani da wannan dama domin mu yaba wa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu kan yadda ya shiga aikin samar da wutar lantarki a jihohin arewa maso yamma da nufin bunkasa tattalin arzikinsu da samar da karin ayyukan yi ga al’ummar jihar Kano.” Inji Gwamnan Jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf a taron manema labarai na hadin gwiwar

Tun da farko kafin taron, gwamnonin sun raka takwaran gwamnan Katsina Dikko Umaru Radda wanda ya tarbi tsohon shugaban kasa Muhammad Buhari domin kaddamar da wani shiri na musamman na tsaro mai taken “Katsina State Community Security Watch Corps (KSWC)”. Gwamnan jihar Katsina ya kuma bayar da tallafin motocin aiki ga jami’an tsaro a jihar

Duk wannan na cikin wata sanarwar da sakataren yaɗa labaran Gwamnan Kano Sanusi Bature Dawakin Tofa a madadin masu magana da yawun Gwamnonin Katsina, Jigawa, Kano, Zamfara, Kebbi da Sokoto

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!