Labarai
Gwamna Dikko Umar Radda ya kai ziyara ƙauyen Sayaya bayan harin Yan bindiga

Gwamnan jihar Katsina Dikko Umar Radda, ya kai ziyara ƙauyen Sayaya da ke ƙaramar hukumar Matazu, bayan wani hari da ‘yan bindiga suka kai a yankin.
Rahotanni sun ce maharan sun kai farmaki ofishin ‘yan sanda inda aka kashe jami’i guda, sannan suka lalata cibiyar kiwon lafiya ta farko tare da kwashe kayayyaki daga shaguna.
A yayin ziyarar, gwamnan ya duba wuraren da aka lalata tare da jajanta wa al’ummar yankin da iyalan waɗanda harin ya shafa.
Haka kuma, ya umarci a tura ƙarin jami’an tsaro domin ƙarfafa tsaro a garin Sayaya.
You must be logged in to post a comment Login