Labarai
Gwamna Fintiri ya kai ziyarar jaje karamar hukumar Lamurde

Gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri ya kai ziyarar jaje karamar hukumar Lamurde biyo bayan wani rikici da ya barke a tsakanin al’ummar garin.
Rikicin dai ya faru ne tsakanin Bachama da Chobo da ya samo asali sakamakon takaddama kan gurin noma.
Rikicin dai yayi sanadiyar rasa rayukan mutane shida tare da raunata wasu da dama da kone rumbuna sama da saba’in harma da lalata gidaje da sace kayan abincin mutanen yakin.
Da yake jawabi kan rikicin, Fintiri ya dauki matakin takaita zirga-zirga na tsawon awanni 24 tare da kai jami’an tsaro wajen da lamarin ya faru kafin daga bisani a sassauta.
Kana a wata ziyarar da ya kai Waduku da Lakan da kuam Rugange, gwamnan ya hore su da su rungumi zaman lafiya da kaunar juna, inda yace babu wata al’umma da zata ci gaba matukar tana fama da rikici.
You must be logged in to post a comment Login