Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Gwamnatin Bauchi ta dakatar da sarkin Misau

Published

on

Gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Muhammad ya dakatar da sarkin Misau, Alhaji Ahmad Sulaiman, biyo bayan rikicin da ya kunno kai a kauyen Hardawa da ke yankin karamar hukumar Misau.

Rikicin dai ya yi sanadiyyar mutuwar mutum tara, tare da jikkata mutane da dama.

Haka zalika gwamnan ya kuma dakatar da dagacin kauyukan Chiroma da Zadawa.

Rahotanni sun ce mutane tara aka kashe yayinda wasu da dama suka jikkata a rikicin da ya barke ranar Litinin.

Wannan ya zo ne bayan danbarwar da ta kunno kai tsakanin manoma da makiyayan Zadawa a yankin karamar hukumar Misau.

A ranar Talata ne gwamnan ya dakatar da mukaddashin shugaban karamar hukumar Misau, Yaro Gwaram, tare da mataimakinsa, Baidu Kafin-Misau da kuma sakatarensa, Usman Abdu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!