Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Gwamna Matawalle ya jagoranci sumame da jami’an tsaro suka kai maboyar ƴan bindiga

Published

on

Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle ya jagoranci wata tawagar jami’an tsaro don kai sumame wata maɓoyar ƴan bindiga da ke birnin Gusau babban birnin jihar.

 

A yayin sumamen rahotanni sun ce jami’an tsaron sun kama wani gawurtaccen ɗan bindiga wanda ya jima yana aikata ta’addanci ga al’ummomin birnin Gusau.

 

Rahotanni sun ce gwamna Matawalle shi da kansa ya rika bai wa jami’an tsaro umarnin yadda za su kai sumame maɓoyar ƴan ta’addar.

 

Harin da ya faru tsakanin ƙarfe 10 zuwa ƙarfe 5 na safiya ya sa jami’an ƴan sanda da jami’an kashe gobara sun yi nasarar cafke da yawa daga cikin ƴan bindigar.

 

Wata majiya da ta fito daga fadar gwmnatin jihar ta tabbatar da cewa gwamnan yasha alwashin fatattakar ƴan ta’adda daga jihar ta zamfara.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!