Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Addini

Sojojin Isra’ila sun kashe Palastinawa 192

Published

on

Rahotanni daga Zirin Gaza na cewa jiragen yaƙin sojin Isra’ila sun ci gaba da yi luguden wuta a birnin a yau litinin.

 

Wannan na zuwa ne kwana guda bayan da firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya bayyana cewa ƙasar sa za ta ci gaba da kai hare-haren kan yankin na Palastinu.

 

Ko a jiya lahadi yayin wani hari da jiragen yaƙin Isra’ila suka kai yayi sanadiyar mutuwar mutane arba’in da biyu.

 

Ya zuwa yanzu dai adadin waɗanda suka rasa rayukansu sakamakon harin da ƙasar ta Isra’ila ke kai wa ta sama ya kai ɗari da casa’in da biyu, ciki har da ƙananan yara hamsin da takwas da kuma mata talatin da hudu

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!