Connect with us

Addini

Gwamna Namadi ya bukaci maniyattan jihar su kiyaye dokokin Saudiyya

Published

on

Gwamnan jihar Jigawa Malam Umar Namadi, ya bukaci maniyatta aikin Hajjin bana da su kasance masu kiyaye dokokin kasar Saudiyya tare da yi wa Najeriya addu’ar  samun zaman lafiya da bunkasar tattalin arziki.

 

Gwamnan, ya bukaci hakan ne lokacin da ya ke yin bankwana da maniyattan 550 da suka tashi a jirgin farko ranar Litinn din makonnan a filin Jirgi na birnin Dutse.

 

Haka kuma, gwamna Namadi,  ya ta ya su murnar samun damar zuwa kasa mai tsarki domin sauke farali ta re da jan hankalinsu kan gudanar da ibada yadda ya dace.

 

Shi kuwa shugaban Alhazan jihar Jigawa mai Martaba Sarkin Kazaure Alhaji Najib Hussaini Adamu, kira ya yi ga maniyyatan da su yi wa Najeriya da shugabanni addu’a yayin ibadar tasu a musamman ma a Harami.

                                      

Maniyatta 930 ne ake sa ran za su sauke farali daga jihar Jigawa a hajjin bana, inda ake sa ran Jirgi na biyu kuma na karshe zai tashi da sauran maniyattan a ranar Alhamis mai zuwa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!