Labarai
Gwamna Radda ya ziyarci garin Mantau da ƴan bindiga suka kai hari

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya ziyarci garin Mantau da ke ƙaramar hukumar Malumfashi da ƴan bindiga suka kashe masallata domin yin ta’aziyya ga iyalan waɗanda suka rasa ’yan uwa a harin.
Wannan na cikin sanarwar da Ibrahim Kaula Mohammed, babban sakataren yada labaran gwamnan, ya fitar ranar Laraba, 27 ga watan Agusta, 2025.
A yayin ziyarar, Gwamna Radda ya bayar da tallafin gaggawa na naira dubu dari biyar ga kowane iyali da abun ya shafa, tare da sanar da shirin gwamnati na gina makaranta da asibiti na zamani, gyaran masallaci da kuma tituna domin bada damar saurin samun taimakon tsaro.
Ya kuma bayyana cewa duk gidajen da aka lalata a harin za a sake gina su.
You must be logged in to post a comment Login