Labarai
Gwamna Zulum ya raba tallafin miliyan 150 ga iyalan sojoji 3 da suka rasu

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya bayar da tallafin naira miliyan 150 ga iyalan jami’an soja uku da suka rasa rayukansu a hare-haren baya-bayan nan da suka faru a jihar.
Tallafin, wanda gwamnatin jihar ta bayar, na daga cikin matakan da gwamnan ke dauka na tallafawa iyalan jaruman da suka sadaukar da rayukansu, da kuma jikkatan da ke cikin aikin yaki da ta’addanci.
A cikin wata sanarwa da kakakin gwamnan, Dauda Iliya, ya fitar, ya ce gwamnan ya kuma mika tallafi ga iyalan dakarun sa-kai da suka mutu yayin aiki, ciki har da samar da guraben karatu ga ‘ya’yansu marayu.
Sanarwar ta ce gwamnan ya ziyarci iyalan marigayi Laftanar Kanal Umar Farouq, da Laftanar Kanal Salihu Iliyasu, da kuma Laftanar Kanal Aliyu Saidu Paiko, domin jajanta musu da kuma nuna alhini kan rashin da suka yi.
A yayin ziyarar da ya kai birnin Abuja, gwamnan ya gana da iyalan marigayi Salihu Iliyasu, inda ya mika sakon ta’aziyya tare da yabawa jajircewarsa wajen yi wa kasa hidima.
You must be logged in to post a comment Login