Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Gwamnan jihar Bauchi ya rushe majalisar zartaswar jihar

Published

on

Gwamnan jihar Bauchi Bala Abdulkadir Mohammed ya rushe majalisar zartaswar jihar nan take.

Haka kuma gwamnan ya sauke Sakataren gwamnatin jihar Alhaji Sabi’u Baba da shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin Dakta Ladan Salihu daga mukamansu.

Hakan dai na cikin wata sanarwa da mai taimakawa gwamnan jihar akan harkokin yada labarai Mukhtar Gidado ya fitar da safiyar yau Labara 9 ga watan Yuni.

Sanarwar ta ruwaito cewa, gwamna Bala Abdulkadir, ya dakatar da dukkan shugabannin majalisar zartaswar jihar da kuma masu bashi shawara.

Sai dai sallama daga aikin ba ta shafi mai ba shi shawara kan harkokin tsaro da mai bai wa gwamnan shawara kan alakar majalisar tarayya da ta jihar da mai ba shi shawara kan harkokin zuba jari da kuma na harkokin yada labarai ba.

Haka kuma sanarwar ta umarci kwamishinonin jihar da su mika aiki ga manyan sakatarorin ma’aikatunsu tare da tabbatar da cewa sun mika dukkan kadarorin gwamnati da ke hannunsu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!