Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Women Handball: Jamhuriyar Congo ta lallasa Najeriya a gasar cin kofin Afirka

Published

on

Kungiyar kwallon hannu ta mata ta Najeriya ta yi rashin nasara a hannun takwararta ta jamhuriyar Congo a gasar cin kafin Afirka na 2021.

An dai gudanar da wasan farko ne a birnin Yaounde dake kasar Cameroon a ranar Talata 8 ga watan Yuni.

A wasanta na gaba, Najeriya za ta kara da kasar Kamarun a gobe Alhamis 10 ga watan da muke ciki na Yuni.

Haka zalika, wannan shi ne karo na farko da Najeriya ta sake fafatawa a gasar tun a shekarar 1994.

Gasar da aka fara a ranar 8 ga watan Yuni, za a karkareta a ranar 18 ga watan Yuni inda kasashe hudu za su samu tikitin zuwa gasar cin kofin duniya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!