Labarai
Gwamnan jihar Ondo ya kori kwamishinonin 3 a gwamnatinsa
Gwamnan jihar Ondo Oluwarotimi Akeredolu ya sanar da cewar ya kori kwamishinonin 3 dake kunshin gwamnatin sa yayin da nada wasu mutum 5 a matsayin sababbin kwamishinoni.
Wannan na kunshe cikin sanarwar da sakataren yada labarai ga gwamnan Mr Olusegun Ajiboye ya fitar a birnin Akure.
Sanarwar ta sanar da sunayen sababbin kwamishinonin da gwamnan Akeredolu ya nada sun hada da Mrs Yetunde Adeyanju da Mrs Titilayo Adeyemi da Mr Temitayo Oluwatuyi da Mr Fatai Olotu da kuma Mr Akindotun
Haka zalika a cewar sanarwar gwamnan jihar ya ce daukar matakin ya zama wajibi wajen yin tankade-da rera, saboda gwamnatin sa na bukatar jajirtattu da za su baiwa jihar ta Ondo gudunmawa.