Labarai
Gwamnan jihar Taraba ya ce gwamnonin kasar nan basu da iko akan jami’an tsaro
Gwamnan jihar Taraba Darius Ishaku ya ce gwamnoni kasar nan basu da iko akan jami’an tsaron kasar nan, duba da cewar ba za su iya bayar da wani umarni ga jami’an tsaron ba.
Darius Ishaku ya bayyana hakan ne a jiya Laraba yayin taron majalisar zartarwar jihar ta Taraba, inda kuma ya karbi bakuncin gwamnan jihar Gombe Ibrahim Dankwambo, wanda ya je jihar domin ta’aziyyar kisan Barista Hosea Ibi yar majalisa mai wakiltar Takun a majalisar dokokin jihar ta Taraba.
Gwamman ya ce da za a baiwa gwamnonin damar iko da jami’an tsaron kasar nan kamar yan sanda da sojoji to da za a samu sauki a bangaren tsaron kasar nan.
Ya kuma ce sunan da ake baiwa gwamnonin jihohi na cewar sune shugabannin tsaro a jihohin su ba tare da basu damar hakan a hukumance ba na iko akan jami’an tsaro ba dai-dai bane.
Tun da farko da ya ke nasa jawabin gwaman dan kwambo ya ce ya kai ziyara jihar ta Taraba ne domin yin ta’aziyya ga rasuwar yar majalisar jihar misis Hosea Ibi bisa kisan da aka yi mata.
Ya kuma ce ziyarar ta zama wajibi duba da alakar da ke tsakanin jihohin biyu