Labarai
Gwamnan Kano ya amince da samar da sabon gidan Ruwa a garin Taluwaiwai, da ke Rano.

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf, ya amince da samar da sabon gidan Ruwa a garin Taluwaiwai, da ke yankin karamar hukumar Rano.
Kwamishinan ma’aikatar albarkatun ruwa Umar Haruna Doguwa ne ya bayyana hakan ya na mai cewa, sabuwar matatar ruwan za ta taimaka wajen magance kamfar ruwa a kananan hukumomin Rano da Kibiya da kuma Bunkure.
A nasu bangaren, shugabannin kananan hukumomin Kibiya da Kura kuma Bunkure, sun yaba wa gwamna Abba Kabir Yusuf,bisa kaddamar da aikin suna mai cewa, hakan zai taimaka matuka wajen magance matsalar ruwan amfanin yau da kullum a yankunan nasu.
Shi ma wani mazaunin yankin karamar hukumar Rano Ibrahim Musa Kahu, ya mika godiyarsa ga gwaman Abba Kabir Yusuf, ya na mai cewa, samar da samuwar matatar zai magance tsawon shekaru su na fuskantar matsalar ruwan sha.
You must be logged in to post a comment Login