Labarai
Gwamnan Kano ya naɗa sabon shugabancin hukumar gudanarwa ta Kano Pillars Fc
Gwamnan Kano Ya Amince Da Nada Sabon shugabancin hukumar Gudanarwa ta Kungiyar Kano Pillars FC Dangane da wa’adin da na baya ya cika a bayan nan.
Wannan na ƙunshe ne ta cikin wata sanarwa da Babban Daraktan yaɗa labaran gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar ya rabawa manema labarai a ranar Lahadi.
Sabbin mambobin hukumar an zaɓo su ne sabo da kwarewa da gogewarsu kuma za su yi aiki na wucin gadi na shekara guda, tare da yuwuwar sabunta su bisa la’akari da kwazon da kungiyar za ta yi a kakar wasanni masu zuwa.
Sababbin shugabannin hukumar sune kamar haka:
– Ali Muhammad Umar (Nayara Mai Samba) – Shugaba – Salisu Kosawa – Honorary Member – Yusuf Danladi (Andy Cole) – Memba – Nasiru Bello – Member – Muhammad Ibrahim (Hassan Yamma) – Member – Muhammad Usman – Member – Muhammad Danjuma Gwarzo – Member – Mustapha Usman Darma – Member – Umar Dankura – Member – Ahmad Musbahu – Member – Rabiu Abdullahi – Member – Abubakar Isah Dandago Yamalash – Daraktan yada labarai – Ismail Abba Tangalash – mataimakin daraktan yada labarai – Engr. Usman Kofar Naisa – Member
Gwamnan ya bayyana kwarin gwiwar sa da cewa wadannan mutane za su zo da sabbin abubuwa da gogewa da za su taimaka wajen tafiyar da harkokin kungiyar ta Kano Pillars FC.
Ana sa ran sabuwar hukumar za ta yi aiki kafaɗa da kafaɗa da ma’aikatar matasa da wasanni ta jiha da sauran masu ruwa da tsaki a harkar wasanni domin bunkasa kungiyar Kano Pillars.
Bugu da kari, gwamnan ya amince da nada Kyaftin din Super Eagles, Ahmed Musa a matsayin jakadan wasanni na jihar Kano.
You must be logged in to post a comment Login