Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

KAROTA : Abinda ya sanya Ganduje ya nada Baffa Babba shugaban kwamiti

Published

on

Gwamanatin jihar Kano ta nada shugaban hukumar KAROTA Baffa Babba Dan Agundi a matsayin shugaban kwamitin kula da hukumar kare hakkin masu sayen kayayyaki ta jihar.

Gwamnan jihar ta Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ne ya tabbatar da nadin nasa, biyo bayan ajiye aiki da tsohon shugaban kwamitin Dakta Yusuf Muhammad Sabo ya yi sakamakon tsayawa takara da ya yi a karamar hukumar Bichi a zaben da ke gabatowa na kananan hukumomi.

Da ya ke mika ragamar aikin  ga sabon shugaban Dakta Yusuf Muhammad ya bayyana gamsuwarsa bisa zabar Baffa Babba Dan Agundi a matsayin wanda zai jagoranci kwamitin, yana mai fatan cewa zai ci gaba da gudanar da ayyuka managarta don samar da kyakyawan sakamakon anan gaba.

Da yake saba layar karbar aikin, Baffa Babba Dan Agundi, ya ce, da ma hukumar KAROTA na yin aiki kafada-da-kafada da hukumar kare hakin masu sayen kayayyaki don haka a yanzu za su kara inganta ayyukansu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!