Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

EFCC ta ayyana neman Yahaya Bello ruwa a jallo

Published

on

Hukumar EFCC, ta ayyana neman tsohon Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ruwa a jallo.

Daukar wannan matakin na zuwa ne sa’o’i kadan bayan da kotu ta dage sauraron karar da hukumar ta EFCC ta shigar sakamakon rashin halartar zaman kotun da tsohon gwamnan ya yi.

Yayin zaman kotun na ranar Alhamis, lauyan EFCC mai suna Kemi Phinro ya faɗa mata cewa “wani mutum da ke da kariya daga tuhuma ne ke bai wa tsohon gwamnan mafaka”.

Tun a baya dai, hukumar ta yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ta na tuhumar Yahaya Bello ne da zargin halasta kudin haram da suka kai naira biliyan 8 da miliya 200.

BBC ta ruwaito cewa, Lauyan hukumar ya bayyana cewa suna duba yiwuwar neman taimakon rundunar soji domin cafke Yahaya Bello.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!