Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Gwamnan kano ya sanya hannu kan dokar naɗa masarautu 3 masu daraja ta 2

Published

on

Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan ƙudirin dokar da ta kafa masarautu uku masu daraja ta biyu a jihar Kano.

Wannan ya biyo bayan tsallake karatu na uku da dokar tayi a majalisar dokoki ta jihar Kano ta gudanar a yau, inda dokar ta ƙunshi masarautun Ƙaraye, wadda zata jagoranci Rogo sai Gaya ta jagoran ci Albasu, Ajingi ita kuma Rano zata jagoranci Kibiya, Bunkure.

Da yake jawabi yayin sanya hannu gwamna Abba Kabir Yusuf ya nan ba da jimawa ba za’a bayyana sunayen sarakunan da za’a tura masarautun domin jagorantar yankin.

kakakin majalisar dokokin jihar Kano Hon Isma’il Jibril Fargore da tawagar sa ne suka jagoranci kawo dakardar ga gwamna domin sanya hannu akan dokar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!