Labarai
Gwamnan Kano ya yi Alla’wadai da rashin halartar kwamishinan ‘yansanda bikin samun ‘yancin kai

Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya yi tur da Allah wadai da matakin da Kwamishinan ƴan sanda na jihar Kano ya ɗauka na ƙin halartar babban bikin cikar nan shekaru 65 da samun ƴancin kai da aka gudanar a filin wasa na Kofar Mata tare da hana jama’i’an ƴan sandan zuwa domin gudanar da fareti.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana hakan ne a yau yayin gudanar da bikin zagayowar samun ƴancin kan ƙasar nan, inda ya nuna rashin jin daɗinsa kan yadda shugaban ƴan sandan kano ya yi watsi da taron da yake da matuƙar muhimmanci ga tarihi da kuma martabar al’ummar ƙasar nan.
Gwamna Abba Ya ce wannan lamari abin takaici ne wanda ba zai taɓa ɓoye wa gwamnati da jama’ar Kano ba, domin hakan ya nuna rashin mutunta al’umma da kuma muhimmancin da taron ya ƙunsa.
Gwamnan ya yi kira ga shugaban ƙasa, Alhaji Bola Ahmad Tinubu, da ya ɗauki tsatstsauran mataki kan shugaban ƴan sanda jihar kano kan wannan al’amari domin kauce wa maimaituwa hakan a nan gaba.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya tabbatar da cewa gwamnatin Kano za ta ci gaba da martaba irin waɗannan taruka domin ƙarfafa haɗin kai da ƙasa da kuma girmama irin rawar da waɗanda suka yi sadaukarwa suka taka wajen ganin an samu ƴancin kai.
You must be logged in to post a comment Login