Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Gwamnati ta samar da mafita wajen dogaro da kai na kasa-Dr Bello Ado

Published

on

Masanin tattalin arziki dake jami’ar Bayero Dr Bello Ado ya  ce bullar cutar Corona ta shafi tattalin arzikin kasar nan,  duba da yadda  hada-hadar kasuwanci ta ragu baya da koma baya da  shigo da kayayyaki daga kasar China ya haifar.

Dr. Bello Ado, ya bayyana hakan ne ta cikin shirin barkada Hantsi da   ya yi duba kan yadda bullar Cutar Corona ta shafi tattalin arzikin kasar nan da sauran bangarori.

Masanin ya kara da cewa ya zama wajibi Najeriya ta dauki matakin magance wannan matsala don kuwa matukar aka ci gaba da dogara da kasashen ketare, wajen tafiyar da harkokin kasuwanci a kasar nan akwai yiwuwar wata rana kasar ta tsaya cik.

Labarai masu alaka.

Coronavirus: Shaguna sun fara daukar matakai a Kano

Covid-19: Masana a Kano sun yi tsokaci kan Coronavirus

Da yake nasa, tsokacin shugaban kungiyar masu hada maguguna ta kasa reshen jihar Kano, Alhaji  Bala Mai Kudi, yace har yanzu ba’a samu maganin da ke warkar da cutar ba ta Corona in da ya shawarci al’umma da su dau matakan da ya kamata don kare kan su daga kamuwa da cutar.

Bakin sun yi kira  ga gwamnati da ta samar da hanyoyin rage dogaro da kayayyakin kasashen ketare, kasancewar dogaro da kasashen waje shi ne ke kawo tarnaki  ga  tattalin arzikin kasar nan da zarar an samu wani tasgaro.

 

 

 

 

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!