Labarai
Ganduje ya taimaka mana da ruwan sha a yankin mu – Mai garin Gama
Mai garin Gama da ke karamar hukumar Nassarawa anan Kano ya koka kan matsalar karancin ruwan sha da suke fuskanta tsawon shekaru ba tare da mahukunta sun kai musu dauki ba.
Mai garin na Gama Alhaji Muhammad Isyaku ya bayyana hakan jim kadan bayan kammala shirn barka da hantsi nan tashar freedom rediyo da ya mayar da hankali kan matsalolin al’ummar yankin.
Ya ce, tuni suka aike da koken su ga Gwamnatin Kano sai dai har kawo yanzu babu wani dauki da aka kawo na magance matsalar ta su.
Shi ma shugaban kungiyar ci gaban Gama Dr Muhammad Shehu Hussain ya ce babban kalubale bai wuce yadda suke fuskantar rashin kyawun hanya da kuma rashin makarantu a kusa wanda hakan ya ke tilasta yaran su yin dogon zango kafin su je makaranta.
Shi ma da ya kasance cikin shirin dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Nassarawa Alhaji Umar Musa Gama ya ce, tuni suka fara wasu ayyuka a karamar hukumar ta Nassarawa ciki harda samar da Asibiti da titi da kuma makarantu.
Alhaji Umar Musa Gama ya kara da cewa, gwamnatin jihar Kano ta ware wasu kudade da za’ayi aikin samar da ruwan sha a yankin, wanda ake sa ran za’a fara aikin nan bada dadewa ba.
You must be logged in to post a comment Login