Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Buhari na ganawa da gwamnoni kan tashin gwauron zabi na kayan abinci

Published

on

Shugaban kasa Muhammdu Buhari na tsaka da ganawa da wasu daga cikin masu ruwa da tsaki kan yadda aka sami tashin gwauron zabi na firashin kayan abinci a kasar nan.

kamfanin dillancin labaru na kasa ya rawaito cewa, daga cikin masu ruwa da tsakin akwai gwamnoni 6 da suka hada da gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu da takwaransa na jihar Lagos Babajide Sanwo-Olu sai gwamnan jihar Jigawa Badaru Abubakar.

Sauran sune  Simon Lalong na Plateau da Darius Ishaku na Taraba da kuma gwamnan jihar Ebonyi Dave Umahi.

Sauran sun hada da gwamnan babban banki na kasa CBN Godwin Emefiele da babban sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha da mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Babagana Monguno.

Buhari zai dakatar da yajin aikin likitoci a Najeriya

Bashir Sanata ya soki Buhari kan mawuyacin halin da ‘yan Najeriya ke ciki

Ana dai gudanar da taron ne a fadar mulki ta shugaban kasa dake Abuja.

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!