Connect with us

Coronavirus

Yadda aka samu karuwar masu dauke da cutar Corona a Najeriya

Published

on

Hukumar dakile yaduwar cututtuka ta kasa NCDC ta tabbatar da karuwar mutane 176 masu dauke da cutar Covid-19, wanda hakan ya kara yawan masu cutar a kasar nan, inda ya kai dubu 55,632 cikin su kuma 43,610 suka warke sai kuma guda 1,070 da suka rasu a dalilin cutar.

Sai dai cikin jerin jihohin da aka sami karin babu jihar Kano, lamarin da ya dora jihar Kano a mataki na 9 cikin jerin jihohin da ke fama da cutar, inda ta ke da yawan mutane 1,728 da suka kamu da cutar cikin su kuma 1, 604 da suka warke sai kuma guda 54 da suka rasa rayukan su, inda a yanzu mutane 70 ne ke jinyar cutar har yanzu.

Makwaftan jihar Kano ma dai wato Jigawa, Kaduna da Katsina ma ba’a sami karin mutanen da suka kamu da cutar ba a jiya, sai dai a yanzu jihar Kaduna na a mataki 6 sai kuma Katsina da ke a mataki na 15 sai Jigawa da ke mataki na 25.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 335,225 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!