Labarai
Gwamnati ta yi kokarin magance cututtukan mata da yara – Sarkin Kano
Mai martaba sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya bukaci ma’aikatar lafiya ta jiha da ta rubanya kokarinta wajen ganin an magance cututtukan da suke damun mata da kananan yara, tare da cutar zazzabin cizon sauro a tsakanin al’umma.
Alhaji Aminu Ado Bayero ya bayyana hakan ne a yayin da ya karbi bakuncin manyan jami’an ma’aikatar lafiya ta jiha karkashin jagorancin kwamishinan ma’aikatar Dakta Aminu Ibrahim Tsanyawa a fadarsa.
Sarkin ya ce ya lura da irin muhimmaci da kokarin da gwamnatin jihar Kano ta ke bayarwa a bangaren lafiya musamman ga al’ummar jihar nan wajen yin rigakafin cututtukan da ke damun al’umma.
Tun da farko da yake na sa jawabin kwamishinan lafiyar Dakta Aminu Ibrahim Tsanyawa ya ce a halin yanzu gwamnatin jihar Kano ta magance lalurar cutar shan inna wato Polio, tare da wasu cutuka masu yaduwa ta hanyar amfani da masu rike da sarautun gargajiya a jihar nan.
A wani labarin kuma, kungiyar Jama’ar Kano Ina Mafita karkashin shugabanta Abdullahi Alhasan, ta kai ziyara ga mai martaba Sarkin Kano, inda ta bayyana masa irin manufofin kungiyar na tallafawa marasa karfi a jihar nan.
Wakilinmu Muhammad Harisu Kofar Nasarawa ya rawaito cewa fadar sarkin a yau ta aiwatar da ayyuka da dama da suka hadar da nadin limaman masallatan juma’a da karbar bakuncin kungiyoyi
You must be logged in to post a comment Login