Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Gwamnati ta zargi kasashen duniya da kin sayawa kasar nan makamai

Published

on

Gwamnatin tarayya ta bukaci manyan kasashen duniya da su daina sauraran karairayi da ake yadawa kan Najeriya, sannan su ki sayarwa da kasar nan makamai na zamani da za a yaki ‘yan ta’adda dasu.

Ministan yada labarai da raya al’adu Alhaji Lai Muhammed ne ya bayyana hakan, yayin zantawa da manema labarai yau a Abuja.

A cewar Alhaji Lai Muhammed akwai bukatar manyan kasashe su taimakawa kasar nan wajen samar da makamai.

Alhaji Lai Muhammed, ya kuma ce, yakar ‘yan ta’adda na bukatar amfani da makamai na zamani saboda haka gwamnati ke kokari don ganin ta samarwa dakarun kasar nan kayan aiki.

Ministan yada labaran da raya al’adu ya kara da cewa, matukar manyan kasashen duniya da suka ci gaba, za su yi kememe su ki sayarwa da kasa makamai na zamani don yaki da ayyukan ta’addanci, to ba daidai bane kuma wadancan kasashe su koma gefe suna korafin cewa, kasar ta gaza wajen yaki da ta ke yi da ta’addanci.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!