Labarai
Za mu bai wa kowanne dan gudun hijira ɗan Borno da yake a Kamaru Naira 500,000 idan ya amince ya koma gida – Gwamna Zulum

Gwamnatin jihar Borno ta sha alwashin inganta tsaro tare da bada kariya ga al’ummar jihar a wani mataki na kara farfado da walwalar jama’a na harkokin yau da kullum
Gwamnan Jihar , Farfesa Babagana Umara Zulum, ne ya bayyana hakan da ya ce gwamnatin jihar sa za ta ba kowane ɗan gudun hijira ɗan Borno da yake a Kamaru Naira 500,000 idan ya amince ya koma gida.
Zulum ya bayyana haka ne yayin da yake jawabi ga ‘yan gudun hijira a sansanin Minawao, da ke yankin Arewa ta Gabashin Kamaru.
Gwamnan ya yi wa al’ummar alkwarin samar da cikakken tsaro a yankunan da za su koma, musamman ma samarwa da jami’an tsaro abinda suke bukata da ƙarfafa tsaron farar hula a Gwoza da sauran yankuna na jihar.
You must be logged in to post a comment Login