Labarai
Gwamnatin Filato ta sanya dokar hana fita ta Sa’o’i 48 a Jos ta Arewa

Gwamnatin jihar filato ta sanya dokar hana fita ta tsawon awanni 48 a karamar hukumar Jos ta Arewa.
Kwamishinar yaɗa Labarai da Sadarwa a jihar Joyce Ramnap, ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da fitar ga manema labarai.
Joyce Ramnap ta ce matakin ya biyo bayan wani hari da ‘yan bindiga suka kai wa al’ummar Angwan Rukuba da ke yankin a daren jiya Lahadi.
Harin, wanda ya faru da misalin karfe 8 na dare ya yi sanadiyyar mutuwar akalla mutane 12, yayin da wasu da dama suka jikkata.
Kwamishinar ta kuma ya yi Allah wadai da harin inda ta yi kira ga mazauna yankin da su kwantar da hankalinsu kuma su bi doka.
You must be logged in to post a comment Login