Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Gwamnatin Kaduna ta saka dokar hana fita a yankin Chikun

Published

on

Gwamnatin jihar Kaduna, ta sanar da sanya dokar hana fita ta tsawon sa’o’i ashirin da hudu a Sabon garin Nassarawa da Tirkaniya a ƙaramar hukumar Chikun.

Gwamnatin ta bayyana hakan ne ta cikin sanarwar da Kwamishinan ma’aikatar tsaro da harkokin cikin gida na jihar Mista Samuel Aruwan ya fitar yau Litinin.

Sanarwar ta ce, “An cimma wannan matsaya ne bisa tabarbarewar doka da oda da ta kai ga kashe wasu mutane biyu a wani rikici da ya ɓarke a garuruwan”.

Sanarwar ta kuma umarci hukumomin tsaro da su aiwatar da dokar hana fita a yankunan, domin dawo da zaman lafiya yayin da ake ci gaba da bincike, don haka gwamnatin jihar ta umarci al’ummar yankunan da su yi biyayya ga dokar hana fita a yankunan wadda ta fara aiki nan take.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!