ilimi
Gwamnatin Gombe na shirin yi wa dalibai karin kudin tallafin karatu

Gwamnan Jihar Gombe, Inuwa Yahaya, ya bayyana cewa gwamnatinsa na shirin ƙara kuɗin tallafin karatu da ake bai wa ɗaliban jihar daga Naira dubu bakwai.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a wara hirar kai tsaye da ya gabatar a kafafen yaɗa labaran jihar da daren ranar Litinin.
Sai dai bai bayyana nawa za a mayar da kuɗin ba, amma ya ce nan gaba kaɗan ɗaliban za su fara ganin sabon sauyin da za a kawo a tsarin bayar da tallafin.
You must be logged in to post a comment Login