Ƙetare
Gwamnatin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ta sake ɗage zaɓen ƙananan hukumomi

Gwamnatin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ta sake ɗage zaɓen ƙananan hukumomi da ta shirya gudanarwa a karon farko cikin shekaru sama da 40.
Mahukunta sun ce zaɓen, wanda aka shirya gudanarwa a ƙarshen watan Agustan wannan shekarar, yanzu zai gudana ne a watan Disamba, tare da zaɓukan ƴan majalisa da na shugaban ƙasa.
Sun ce dalilin sake ɗaga wannan zaɓe dai shi ne rashin isassun kuɗaɗe da kuma matsaloli na wasu kayayyaki da ake buƙata domin gudanar da zaɓen.
A halin da ake, mambobin jam’iyyar adawa na kira da a sake fasalin hukumar zaɓen ƙasar, tare da neman tattaunawa da shugaban ƙasar, Faustine ArchangeTouadéra.
Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya na fama da rikici ne tun a shekarar 2013, lokacin da ƴan tawaye suka ƙwace ragamar mulkin ƙasar, kana suka tilasta wa shugaba na wancan lokacin, Francoise Bozize sauka daga mukaminsa.
You must be logged in to post a comment Login