ilimi
Gwamnatin Jigawa na shirin kashe sama da miliyan Dubu 67 wajen inganta ilimi

Gwamnatin jihar Jigawa, ta ce, ta shirya kashe sama da Naira miliyan dubu 67 wajen inganta harkokin ilimi matakin farko.
Kwamishinan ma’aiktar ilimi a matakin farko Dakta Lawan Yunusa Danzomo, ne ya bayyana haka a taron gwamnati da Jama’a karo 20 a kananan hukumomin Gwaram da Roni.
Haka kuma, ya kara da cewa, gwamnatin jihar ta yi ayyukan gyara da gina sabbin Ajujuwan makarantu da bayar da horo ga malamai da daukar wasu sababbi.
Da ya ke jawabi, shi ma babban mai taimaka wa gwamna na musamman kan harkokin dalibai Ambasada Salisu Muhd, ya ce, gwamnatin jihar ta samar wa matasa yan asalin karamar hukumar Roni guda 59 guraban karatu a jami’o’in Najeriya daban-daban a cikin shekaru 2.
Haka kuma, ya kara da cewa a kowace shekara adadin daliban da ke samun damar yin karatun lafiya na karuwa kamar yadda a wannan shekarar da muke ciki kadai an samu akalla dalibai sama da 90 daga karamar hukumar ta Roni.
You must be logged in to post a comment Login