Connect with us

Kiwon Lafiya

Gwamnatin Jigawa ta biya fiye da naira biliyan 5 hakokin ‘yan fansho

Published

on

Gwamnatin jihar Jigawa da hukumar kula da ‘yan fansho ta jihar sun biya fiye da Naira biliyan 5 hakokin ‘yan fansho na shekara guda.

Babban sakatare a hukumar Alhaji Ahmad Fagam ya sanar da hakan ga manema labarai a birnin Dutsen a jiya Litinin.

Alhaji Ahmad Fagam ya ce gwamnatin jihar ta ce lokaci yayi ta biya ‘yan fasnho hakokin su na shekara ta 2018 wandanda suka yi ritaya daga aiki.

Babban sakataren ya kara da cewar, hukumar ta ‘yan fasnho ta biya ‘yan fansho hakokin su na farkon watannin 6 na shekara daga watan Janairu zuwa Disamba na duk wata.

Yayi bayanin cewar kudin ya hada da wadanda suka yi ritaya da na kananan hukumomi da na kuma sashin ilimi na kananan hukumomin na jihar ta Jigawa.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!