Labarai
Gwamnatin Jigawa ta gyara wutar lantarkin garuruwa 9 bayan lalacewar fiye da shekaru 10

Gwamnatin jihar Jigawa ta gyara wutar lantarkin wasu garuruwa 9 bayan lalacewar da ta yi sama da shekaru 10 a yankin karamar hukumar Kirikasamma.
Haka kuma, gwamnatin ta kashe sama da naira miliyan dubu 30 wajen yin aiyukan hanyoyi a sassan yankin cikin shekaru biyu.
Gwamna Malam Umar Namadi ne dai ya bayyana haka ya yin taron gwamnati da Jama’a karo na 22 a karamar hukumar ta Kirikasamma.
Kananan hukumomi 5 ne dai suka rage a wannan shiri na gwamnati da Jama’a, wadda suka hada da Taura a masarautar Ringim sai ‘Yan-kwaahi a masarautar Kazaure.
Sauran su ne karamar hukumar Miga a Masarautar Dutse da kuma Sule-Tankarkar a yankin Gumel sai Malamadori a masarautar Hadeja.
You must be logged in to post a comment Login