Jigawa
Gwamnatin Jigawa ta kashe Biliyan 25 wajen yin hanyoyi Kiyawa cikin shekaru 2

Gwamnatin jihar Jigawa ta kashe Naira miliyan dubu 25 wajen yin aiyukan hanyoyi a karamar hukumar Kiyawa cikin shekaru 2.
Kwamishinan ayyuka da Sufuri Injiniya Gambo Shuaibu Malam, ne ya bayyana haka a taron gwamnati da Jama’a na karamar hukumar Kiyawa.
Ya ce, daga cikin aiyukan da aka yi da kudin har da gyaran hanyoyin da Ruwa ya lalata da kuma gina sabbi.
Haka kuma, kwamishinan ya kara da cewa, an bayar da kwangilar aikin sabuwar hanyar da ta tashi daga Andaza zuwa Dangoli zuwa Katanga mai tsawon kilomita 17 kan kudi sama da Naira miliyan dubu 2.
Dangane da matsalar ambaliyar Ruwan da ke addabar garin Kiyawa a kusan duk shekara kuwa, kwamishinan ya ce za a dakile dalilan da ke haddasa matsalar kafin Damunar badi.
You must be logged in to post a comment Login