Jigawa
Gwamnatin Jigawa ta kashe fiye da Biliyan 4 wajen samar da titia a Sule-Tankarkar

Gwamnatin jihar Jigawa ta ce, ta kashe sama da Naira miliyan dubu 40 wajen yin aikin samar da hanyoyin mota a karamar hukumar Sule-Tankarkar a cikin shekaru biyu.
Da ya ke jawabi a wurin bikin bude aikin hanyar Babban Sara zuwa Sabaru zuwa Albasu da ke yankin karamar hukumar, gwamna Malam Umar Namadi, ya ce, gwamnatinsa na samar da Titina ne domin rage wa manoma da ‘yan kasuwa da sauran al’umma wahalar sufiri.
Haka kuma, gwamnan ya ce, sabuwar hanyar Burjin ta babban-Sara ta shafi a kalla garuruwa 50 da ke yankin.
Da ya ke jawabi yayin taron, kwamishinan aiyuka na jihar Injiniya Gambo Shu’aibu Malam, ya ce, an bada kwangilar aikin hanyar ne kan kudi Naira miliyan dubu 4 da miliyan 400.
You must be logged in to post a comment Login