Labarai
Gwamnatin Jigawa ta kashe sama da miliyan dubu 3 wajen samar da hasken wutar lantarki a jihar

Gwamnatin jihar Jigawa ta kashe sama da Naira miliyan dubu 3 wajen samar da hasken wutar lantarki a karamar hukumar Dutse, kasa da shekara guda kacal.
Da yake jawabi a gurin taron gwamnati da Jama’a karo na 9 a karamar hukumar Dutse, kwamishinan wutar lantarki Injiniya Dakta Suraja Musa ya ce daga cikin ayyukan da Sabuwar ma’aiktarsa ta yi sun hada da sabin ayyuka da gyare-gyaren kayan samar da wutar.
Kazalika Dakta Suraj ya kara da cewa birnin Dutse yafi ko ina samun aikin wuta mai yawa kasancewarta hedkwatra jihar kuma ta Karamar hukuma.
Shima kwamishinan ayyuka da sifiri Injiniya Gambo Shuaibu Malam, ya ce nan gaba kadan gwamnatin jihar za ta fara aikin tagwayan titi zuwa Fadar mai Martaba Sarkin Dutse bayan kammala wasu sabin hanyoyin mota masu yawa birnin Dutse.
You must be logged in to post a comment Login