Labarai
Gwamnatin Jigawa ta rike albashin Malaman Firamare 239

Gwamnatin jihar Jigawa ta rike albashin malaman makarantun Firamare guda 239 sakamakon rashin zuwa aiki da basayi.
Shugaban hukumar ilimin bai daya na jihar Farfesa Haruna Musa ne ya bayyana hakan a zantawar sa da manema labarai, jim kadan bayan kammala horar da malaman dake koyarwa a makarantun Arabiya sy 250.
Haruna Musa ya kuma ce, malaman an samu malaman da kin zuw makarantun su na tsawon watanni biyu, wasu har shekaru uku hakan ne yasa aka dauki matakin a kan su.
Ya kuma ce da yawa daga cikin wasu malaman sunakin zuwa aiki na tsawon lokaci kuma suna karbar albashi duk wata.
You must be logged in to post a comment Login