Labarai
Gwamnatin Jigawa ta sanya Naira 10,000 a matsayi Alawus ga masu Unguwanni

Gwamnan Jihar Jigawa Malam Umar A Namadi ya amince da ƙarin alawus alawus na masu unguwanni a fadin jihar Jigawa daga naira dubu uku zuwa naira dubu goma a wata.
Hakan na zuwa ne bayan taron majalisar zartarwar jihar da aka gudanar a gidan gwamnati da ke Dutse.
Kwamishinan Muhalli da Sauyin Yanayi na jihar, Dokta Nura Kazaure, ya ce ƙarin alawus ɗin na daga cikin matakan da gwamnatin jihar ke ɗauka domin nuna kulawa ga shugabannin gargajiya a matakin ƙasa, waɗanda ke taka muhimmiyar rawa wajen tafiyar da harkokin al’umma da kuma aiwatar da manufofin gwamnati.
A taron majalisar, an kuma amince da aika kudiri zuwa ga majalisar dokokin jihar ta Jigawa domin kafa Jami’ar Kimiyyar da Harkokin Lafiya, domin bunkasa fannin a fadin jihar.
You must be logged in to post a comment Login