Labarai
Gwamnatin Jigawa ta yi wa Alkali Ritaya bisa samunsa da laifi

Hukumar Kula da Ma’aikatan Shari’a ta Jihar Jigawa ta amince da yin ritayar dole ga alkalin Kotun Shari’a, Sadisu Muhammad Haruna, bisa samunsa da laifin nuna rashin da’a a aiki.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Daraktan yada Labarai na hukumar, Abba Wangara, ya fitar a Dutsen jihar.
Hukumar ta ce bayan nazari kan korafin da Abdullahi Hamza ya shigar da kuma hujjojin da aka gabatar, ta samu alkalin da laifin karbar kudade ba bisa ka’ida ba da kuma tsare mai kara ba bisa doka ba.
kumar ta bayyana cewa wannan aiki na karbar kudade ta haram da kuma tsare mutum ba bisa ka’ida ba babban saba wa ka’idojin aikin shari’a ne da kuma cin zarafin mukami.
Baya ga haka, hukumar ta kuma amince da karin girma ga ma’aikata sama da 80 a matakai daban-daban.
You must be logged in to post a comment Login