Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Gwamnatin jihar Bauchi ta amince da ritayar mataimakinta

Published

on

Gwamnatin jihar Bauchi ta amince da ritayar da mataimakin gwamnan jihar injiniya Nuhu Gidado ya yi inda kuma ta yi masa fatan alheri a rayuwar sa ta gaba.

 

Wannan na kunshe cikin wata sanarwa da mashawarcin na musamman kan kafafen yada labarai ga gwamnan jihar ta Bauchi Ali M Ali ya fitar da safiyar yau.

 

Sanarwar ta ruwaito Gwamman jihar ta Bauchi Alhaji Muhammad Abdullahi Abubakar na bayyana tsohon mataimakin gwamnan a matsayin wanda ya sauke nauyin da aka dora masa, a don haka ya cancanci dukkan yabo daga gwamnatin jihar da ma al’ummar jihar baki daya.

 

A jiya ne dai mataimakin gwamnan sanar da murabus din nasa cikin wata wasika da ya fitar mai dauke da kwanan watan 16 ga watan Mayun da muke ciki, bisa wadansu al’amura da suka sha kan sa da ya ga cewar ya kamata yayi murabus daga kan mukamin nasa.

 

Sai dai wani makusancin gwamnan ya shaida manema labarai cewar rashin fahimtar juna ce tsakanin sa da gwamnan ta sanya shi yin murabus din.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!